Home

Assalamu alaikum warahmatullah.
Ina maku barka da shigowa shafin horaswa na Marnaf Global DIY.
Haƙiƙa Marnaf ta na da hadafi na kawo wannan tsari sannan tana da tulin shawarwari ne ga ƴan!uwan ta matasa.
Da farko idan muka duba halin da matasan ƙasar mu ke ciki musamman na arewa ba ƙaramin abun baƙin ciki bane.
 A taƙaice zan yi bayanin nan,buri na in samu haɗin kan wasu daga cikin ku domin mu tsaya da ƙafafunmu,mu girme ma zaman banza da bangar siyasa.
Marnaf Global DIY yana tafiya ne a kan tsarin kasuwancin da ake kira mai dogon zango.
Tsari ne wanda mutum kan sha wuya matuka da faɗi tashi kafin ya cimma gachi,amma da damar damar ta samu kuma shikenan.
Buri na na farko a cikin wannan tsari shi ne,mutanen ƙasa ta su san akwai wani abu CREACTIVITY(hanyar da kan samar ma mutane sauƙi domin iya sarrafe-sarrafe) 
Na biyu shi ne su fahimci abun,sun san akwai ababen da ake sarrafawa na kusa da su a da marasa amfani amma yanzu ance za su yi amfani,to su fara fahimtar gaskiyar hakan.
Na uku shine su fara ƙarɓar abun,daga nan ne za su fara tunanin gwadawa,da hakan ta faru burin wannan kamfani ya cika.

Ku sani mai wannan yunƙuri duk da mace ce wadda bata mallaki komai ba,amma ƙarfin burin da zuciyar ta ke da shi na ganin matasan ƙasarta sun daina kukan rashin aiki sun fahimci wane aikin ne ma ya kamace su,yasa ta ke mafarkin wannan tafiya da ta fara a wayi gari ta samar da danƙareren kamfani da za a ji amon ayyukan sa har a ƙasashen ƙetare.

Shin akwai wanda /wadda ta shirya bada hannu domin ta samu aiki me cikakkar offer?
Ko kun san ina da tanajin da zamu fara taimakon kammu dan samun kuɗaɗen da za mu fara ƙarfafa wannan tafiya a jahohin mu na arewa?kukan da zuciya ta ta ke shine na san raunin matasan ƙasa ta,ina Addu’a Allah yasa kada ku bani kunya.
Albishir na farko da zan fara muku shi ne,duk wanda ya ke ganin yana da sha’awar haɓaka hakan to zai zamo wakili ne na jihar sa tsawon yadda Allah zai ɗaukaki abun.
A cikin duk abubuwan da zamu koya ina son mu dinga sharing ideas tare da ku,ni ma ba gwana bace,ta iya yuwuwa wasu cikin ku su zarce fikrar da na ke da ita da kaso hamsin ma,amma ta yaya za su gane hakan?
Ta hanyar gwada abinda suka koya da janza ma abun tsari da na su tunanin,na san kuna da baiwa dan Allah ku jaraba ta a nan mu gani mu ƙaru da juna.
Idan da masu tambaya ina jira,kafin in sako abubuwan da za su fara nema dan darussan da za mu yi.